30 Satumba 2021 - 13:20
Takadamar Visa : Aljeriya Ta Kirayi Jakadan Faransa

Ma’aikatar harkokin wajen Aljeriya ta kirayi jakadan Faransa a kasar, kwana guda bayan da Faransa ta sanar da daukar tsauraren matakan bada takardar visa, ga ‘yan Ajeriyar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Aljeriya ta bayyana wa jakadan na Faransa, cewa sam bata ji dadin matakin na mahukuntan Paris ba na rage yawan ‘yan Aljeriya da ake baiwa Visa ba, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta sanar.

A ranar Talata ne, Kasar Faransa ta sanar da tsaurara matakan bada takardar shiga kasar ta Visa, ga ‘yan kasashen Morocco, Aljeriya da kuma Tunisia.

Matakin ya tanadi rage bada visa ga ‘yan kasashen da kashi hamsin cikin dari ga ‘yan Aljeriya da Morocco, sai kuma kashi talatin cikin dari ga ‘yan kasar Tunisia.

Saidai kasashen Aljeriya da Morocco sun ce sam matakin bai dace ba.

Faransa ta ce ta dauki matakin saboda yadda kananen ofisohin jakadancin kasashen basa baiwa mutanensu dake zuwa ci rani a faransa takardun da zasu basu damar komawa gida.

342/